Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barr Ya Kare Matakin Tura Jami'an Tsaron Tarayya Zuwa Garin Portland


Antoni janar na Amurka William Barr ya kare matakin aikawa da daruruwar ma’aikatan tarayya zuwa Portland na jihar Oregon da wasu wurare domin shawon kan zanga zanga da tashin hankali, yayin da ‘yan adawa na Democrat suke zargin sa da cin zarafin bil Adama ga masu zanga zangar lumana.

Wannan ne karon farko da Barr ya bayyana gaban kwamitin shari’a na majalisar wakilai da Democrat ke da rinjayi a matsayin sa na antoni janar, inda ‘yan Democrat din suka zarge shi bisa wannan mataki da ya dauka a Potland domin taimakawa yunkurin shugaba Donald Trump na sake zaben sa a watan Nuwamba.

Barr ya bada bahasi tsawon sa’o’i biyar a cikin matsi a dakin sauraren bahasi da ya cika makil da jama’a, inda ‘yan Democrat suka bayyana matukar fushin su ga wannan mataki kana su ma ‘yan Republican suna nuna damuwa game da yadda ake hana Barr damar bada bayanai.

Barr ya ce mutuwar George Floyd a hannun farar fatar ‘yan sanda a karshen watan Mayu a Minneapolis babban abin damuwa ne, lamarin da ya yi sanadiyar sake duban alakar jami’an tsaron farar fata da bakar fatar Amurka a cikin kasar.

Amma ya ce zanga zangar ta Portland da na wasu wurare basu da wata alaka da mutuwar Floyd.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG