Accessibility links

Batun Sunayen Ministoci Da Aka Kaiwa Buhari


Buhari transition team, Abuja, April 29, 2015.

Akan cece kuce da akeyi kan shugaba mai jiran gado Muhammadu Buhari ya dage kan cewa babu wanda yake da ikon nada masa ministoci kamar yadda shima ba zai yi shishshigi wajen nada kwamishinoni a jihohi ba.

Domin jin gaskiyar batun Hajiya Jummai Ali ta zanta da Direktan hulda da manema labaru da jama’a na shugaban Mallam Shehu Garba.

Wanda ya musunta wannan labari inda yace ba zai iya cewa haka labarin yake ba, kamar yadda aka fito da wannan magana ana nunin cewa ko akwai wani rashin amincewa da juna tsakanin shugaban kasa da gwamnoninsa harma da shugabannin jam’iyya a wani bangaren wannan kuwa ba haka yake ba.

A wata hira da zabebben shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da wasu gidajen jaridu dai yace baya son a saka masa baki wajen nade naden ministocin sa daga gurin gwamnoni, saboda yayin da gwamnoni suka zo nada kwamishinoninsu basa tuntubar shugabannin kananan hukumomi suna yin abin gabansu kawai, kuma bai kamata ba su saka masa baki a nasa ba.

A baya dai tsari ne na jam’iyyar PDP idan baka fito ta hannun gwamna ba mutum bai isa ya zama minister ba.

XS
SM
MD
LG