Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Takarar Musulmi Da Musulmi Na Ci Gaba Da Daukan Hankulan Jama'a A Najeriya


Batun Tikitin Takaran Musulmi Da Musulmi Yana Ci Gaba Da Daukan Hankali A Najeriya
Batun Tikitin Takaran Musulmi Da Musulmi Yana Ci Gaba Da Daukan Hankali A Najeriya

Batun tikitin takarar Musulmi da Musulmi na ci gaba da daukan hankali a Najeriya musammana a Arewacin kasar inda kungiyoyin addini ke cewa ba shi ne mafita ba.

ABUJA, NIGERIA - Wasu limaman manyan addinan kasar guda biyu wato Kiristoci da Musulmi sun yi wani taron manema labarai a Abuja, inda suka bayyana mafita.

A daidai lokacin da Jam’iyyar APC mai mulki ke ci gaba da neman wanda za ta tsayar a matsayin mataimakin ‘dan takararsu, mabiya addinai manya guda biyu Muslmi da Kiristoci na kira da babbar murya da a yi takatsantsan wajen nemo wa Bola Ahmed Tinunbu mataimaki.

A lokacin da ya ke bayyana damuwarsa ga manema labarai, Bishop Edward Williams Chanomi, na Majami'ar Prince Chapel International Church da ke Abuja, ya yi tsokaci cewa tun da farko a Najeriya idan an yi shugaba Musulmi to Kirista ne mataimakinsa, saboda haka bai kamata a canza tsarin ba yanzu.

Shi ma tsohon mai ba Gwamnan Jihar Kaduna shawara a harkokin addini da aikin hajji, Halliru Abdullahi Maraya, yana ganin tsayar da ‘yan takara mabiya addini daya ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.

Llokacin da ya ke tsokaci akan batun tsohon shugaban matasan Kiristoci kuma sakataren Kungiyar Arewa Transformational leaders, Pastor Simon Dolly, ya ce akwai abin dubawa a irin wannan mataki da Jam’iyyu ke kokarin yi a gabanin zaben shekara 2023.

Kungiyoyin addinan biyu sun ce kalubalantar wannan mataki na tsayar da ‘yan takara daga addini iri daya, ya nuna suna kishin ci gaban kasar da al'ummar ta ne baki daya, domin yin haka ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

Batun Tikitin Takarar Musulmi Da Musulmi Na Ci Gaba Da Daukan Hankulan Jama'a A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

XS
SM
MD
LG