Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BAUCHI: Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje da Dukiyoyi a Misau da Darazo


Wasu da ambaliyar ruwa ya raba da gidajensu
Wasu da ambaliyar ruwa ya raba da gidajensu

Ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyar lalata daruruwan gidaje da konaki a yankunan kananan hukumomin Misau da Darazo

Bayanai daga hukumomin yankunan sun ce ruwan saman sun malale kan tituna suka kuma rusa gidaje.

Ado Sarkin Aska mai rike karamar hukumar Misau yace ruwan ba cikin garin aka yi ba. An yi ruwan saman ne a wuraren dake makwaftaka da Misau amma ya malale zuwa cikin garin

Kawo yanzu gidaje 197 ne ruwan ya cinye a Misau. Akwai wani kauyen kuma da ruwan ya shafi gidaje 20. Kauyuka ma dake kusa da garin ambaliyar ta shafesu.

Shi ma mai rikon karamar hukumar Darazo Malam Mustapha Zailani yayi bayani.Tun karfe shida na yamma aka fara ruwan sama a gari har zuwa wayewar gari. Ruwan ne ya dinga kwalale ya shiga gidaje mutane.

Ruwan yayi barna matuka har ma sun kafa kwamiti dake bi gida gida yana suna rubuta sunayen mutanen da ambaliyar ta shafa.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG