Farkon kama aikin gwamnoni musamman sabbi na cike da bayanan gadon dimbin bashi tare da koke akan irin ta'adin da gwamnatocin baya suka tafka, musamman wai gwamnonin PDP.
Yanzu da suka kwashe wata shida suna mulki shin wane irin hali suke ciki. Shin sun soma murmurewa ko da sauran zazzabi a jikinsu.
Gwamnan Bauchi Barrister M.K. Abubakar a wani taron hadin gwuiwa a Abuja ya yiwa Allah godiya da abun dake faruwa yanzu a Bauchi. Yace mafi yawan 'yan jiharsa suna cikin farin ciki da walwala. Bauchi jihar masu aikin albashi ne idan ba'a biya albashi ba zai shafi kasuwanci da tattalin arzikin jihar. Idan an biya albashi jihar sai ta farfado.
Gwamna Abubakar yace tun daga zuwan gwamnatinsa ya dauki kudurin tabbatar da biyan albashi lamarin da ya sa ya nemi lamuni domin biyan albashin farko. Jihar na anfani da agajin da ta samu daga gwamnatin tarayya a dinga biyan albashi kan lokaci.
A hedkwatar PDP tsohon kwamishanan PDP daga Kaduna Dr Saidu Abdullahi wanda ya nuna da gangan APC ke kushe PDP. Yace mutane sun soma nadama domin bayan watanni shida da gwamnatin ta yi babu wani abun a zo a gani.Jam'iyyar PDP ta yi rawar gani saidai idan ana son a cigaba da yin karya.
Masur Mani Soro yana cikin wadanda suka tallata APC a Bauchi har ta lashe gwamnati.Akan ko gwamnonin APC sun shirya yace ya san nashi gwamnan ya shirya tsaf tun lokacin da suke fafutikar neman zabe.
Ga karin bayani.