Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kogi: APC Na Nazari Akan Rasuwar Dan Takararta Domin Bayyana Matsayi


APC LOGO
APC LOGO

Rasuwar dantakarar jam'iyyar APC kafin a kammala zabe abu ne da bai taba faruwa ba soboda haka kowa na fadin albarkacin bakinsa abun da za'a yi amma jam'iyyar tace tana nazari kuma zata bayyana matsayinta akan lamarin.

Jam'iyyar APC tace rashin da aka yi babban rashi ne ga Najeriya baki daya.

Jam'iyyar ta mika ta'aziyarta ga iyalan marigayi Abubakar Audu da abokansa da al'ummar jihar Kogi da ma Najeriya.

Bisa ga rasuwarsa jam'iyya tana nan tana nazari akan ainihin furucin shugaban shirya zaben jihar yayinda akan cewa ba'a kammala zaben ba. Yace bayan nazari jam'iyyar zata fitar da matsayinta.

Amma jam'iyyar ta yabawa hukumar zabe da yadda zaben ya gudana ranar Lahadi. Ma'aikatan hukumar zabe da jami'an tsaro duk sun taka rawar gani.

Akan ko jam'iyyar APC ka iya rasa kujerar saboda rasuwar dan takararta sai mai magana da yawun jam'iyyar yace wannan ba zai faru ba domin jihar ta karbi jam'iyyarsu. Wakilansu dake majalisun tarayya duk 'yan APC ne haka ma lamarin yake a majalisar dokokin jihar. Banda haka kowa ya ga kamun ludayin shugaba Buhari.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG