Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayanai Marasa Kyau Ne Suka Haddasa Harin Garin Rann - Irabor


Harin da sojojin Najeriya suka kai bisa kuskure kan sansanin 'yan gudun hijira.
Harin da sojojin Najeriya suka kai bisa kuskure kan sansanin 'yan gudun hijira.

Wani hafsa a rundunar sojojin Najeriya yace harin da aka kai bisa kuskure akan sansanin 'yan gudun hijira a yankin arewa maso gabashin kasar, ya auku ne saboda bayanai da ba dai-dai ba.

Manjo Janar Leo Irabor, ya gayawa tawagar wakilan kwamitin sulhu na MDD da suka kai ziyara yankin jiya Lahadi cewa, harin da jirgin yakin kasar ya kai ranar 17 ga watan Janairu a garin Rann, har ya halaka farar hula 236 "mummunar kuskure ne " da bayanai marasa kyau suka haddasa.


"Bayanai da aka samu sun nuna akwai 'yan Boko Haram a kusa da inda aka kai harin,"sai dai bayanai da aka bayar sun saba da hakikanin lamarin."
Janar Irabor ya ci gaba da cewa koda shike ba wai yana kokarin kare kuskuren da aka yi bane, domin kwanaki biyu bayan kuskuren nan, 'yan Boko Haram din sun kai kan garin dake jahar Barno, inda nanne cibiyar kungiyar ta Boko Haram.


A lokacin harin da jirgin yakin Najeriyan ya kai hari kan sansanin 'yan gudun hijirar ana raba kayan masarufi, kuma harin bama-bama biyu da jirgin ya jefa akansu ya rutsa da mata da kuma yara, cikinsu har da ma'aikatan reshen kungiyar agaji na Najeriya dama 'yan kungiyar na kasa da kasa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG