Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kokarin Shiga Tsakanin Buhari Da Osinbajo


Buhari da Osinbajo

A karo na biyu fadar shugaban Najeriya ta ce bata jin dadin yadda wasu ‘yan tsiraru ke son shiga tsakanin shugaba Mohammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Osinbajo, bisa ci gaban da ake samu a kasar.

Mai baiwa shugaban ‘kasa shawara kan harkokin siyasa Sanata Babafemi Ojudu, yace sun lura da cewa wasu ‘yan ‘gaza gani’ sun dage sai sun shiga tsakanin shugaban Buhari da mataimakinsa, bayan kuwa shugaban da mataimakinsa duk abu ‘daya ne.

Kwararre kan sha’anin aikin gwamnati ‘Dan Masanin Fika, yace dalilin da yasa ake ganin abubuwa na faruwa ta hannun Osinbajo, saboda a baya su biyu ne kowa yana yin aikinsa, yanzu kuwa baki ‘daya ayyukan suna hannun Osinbajo domin Buhari baya nan. Ya kuma ‘kara da cewa wannan lamari ne na siyasa domin su nuna cewa yafi maigidansa kazar-kazar.

Sai dai kuma ‘dan jaridar da ya fara takalo wannan muhawara Mohammad bin Ibrahim, bai gamsu da duk ire-iren bayanan da kusoshin gwamnatin ke yi ba. inda ma yake ganin Buhari ba zai iya yin kazar-kazar din da Osinbajo yake yi a yanzu ba, haka zalika umarnin da mataimakin yake bayarwa irin wanda ya baiwa babban bankin kasar don karya darajar dalar Amurka.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG