Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bazoum Ya Nemi A Kai Masa Dauki


US Africa Summit
US Africa Summit

“Ina kira ga Amurka da daukacin kasashen duniya, su taimaka wajen maido da doka da oda a Nijar." Bazoum ya ce cikin makalar da ya rubuta.

Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa a Jamhuriyar Nijar, ya nemi Amurka da sauran kasashen duniya su kai masa dauki.

Cikin wata makala da ya rubuta wacce aka wallafa a jaridar Washington Post, Bazoum mai shekaru 63, ya ce bai ga dalilin da ya sa sojojin suka karbe madafun iko ba.

“Ina kira ga Amurka da daukacin kasashen duniya, da su taimaka wajen maido da doka da oda. Al’umar Nijar ba za su taba mantawa da taimakon da za ku musu a wannan muhimmin lokaci ba a tarihin kasar.

Janar Tchiani, dama
Janar Tchiani, dama

“Wannan juyin mulki da wani bangaren sojoji suka yi wa gwamnati a ranar 26 ga watan Yuli ba shi da tushe balle makama.

“Idan har suka yi nasara, hakan zai haifar da mummunan sakamako ga Nijar, yankinmu da duniya baki daya.” Bazoum ya ce cikin makalar wacce aka wallafa a ranar Juma’a a jaridar ta Washington Post.

Bazoum ya kara da cewa, babu gaskiya a ikrarin da sojojin suka yi na cewa, tsaron kasar ta Nijar ya tabarbare.

Masu zanga-zangar goyon bayan juyin mulki a Nijar
Masu zanga-zangar goyon bayan juyin mulki a Nijar

“Suna ikirarin cewa yakin da muke yi da masu ikirarin jihadi ba ya nasara, sannan matakan da muke dauka don bunkasa tattalin arzikinmu da sauran tsare-tsare da kawancenmu da Amurka da kasashen turai yana mummunan tasiri akan kasarmu.

“Hasali ma, tsaro ya inganta a Nijar, kashi 40 na kasafin kudinmu tallafin ne daga kasashen waje, amma hakan ba zai samu ba idan har wannan juyin mulki ya yi nasara.” Bazoum ya ce.

A cewar Bazoum, a kudancin Nijar da ake fama da mayakan Boko Haram, an kwashe shekaru biyu ba tare da an samu wani hari ba, sannan ‘yan gudun hijira na ta komawa kauyukansu.

Bazoum ya kuma yi gargadin cewa Rasha da sojojin haya na Wagner za su iya yin kaka-gida a yankin idan har juyin mulkin ya dore.

Dakarun Faransa a Nijar
Dakarun Faransa a Nijar

Sojojin da suka yi juyin mulki karkashin Janar Abdourahamane Tchiani, sun ce sun karbe ragamar mulkin kasar ne saboda al’amuran tsaro na tabarbarewa a kasar, sannan matakan da ake dauka don bunkasa fannin tattalin arziki ba sa aiki.

Kasashen duniya da dama sun yi Allah wadai da wannan juyin mulki yayin da kungiyar ECOWAS/CEDEAO, da kungiyar hadin kan Afirka ta AU da ma Majalisar Dinkin Duniya, suke kira da a gaggauta sakin Bazoum tare da mayar da kasar bisa turbar Dimokradiyya.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad III, (hagu) Shugaba Tinubu, (tsakiya) Janar Abdulsalami, dama (Hoto: Facebook/Buharist Reporters)
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad III, (hagu) Shugaba Tinubu, (tsakiya) Janar Abdulsalami, dama (Hoto: Facebook/Buharist Reporters)

A makon da ya gabata kungiyar ta ECOWAS/CEDEAO ta kakaba takunkumai akan kasar ta Nijar tare da yin barazanar daukan matakin soja idan masu juyin mulkin suka ki mika wuya.

A ranar Alhamis wata tawagar wakilan ECOWAS/CEDEAO karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta isa Yamai a wani mataki na shiga tsakani a rikicin juyin mulkin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG