Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Goyon Bayan Juyin Mulki Sun Yi Gangami A Nijar


Masu zanga zanga a Nijar
Masu zanga zanga a Nijar

Gangamin har ila yau na zuwa ne yayin da kasar ta Nijar take cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai daga Faransa.

Daruruwan masu zanga-zanga a Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da gangamin ci gaba da nuna goyon bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

Yayin gangamin, an ga masu zanga-zangar rike da tutocin Rasha, suna rera wakokin kyamatar Faransa da sauran kasashe da ke adawa da juyin mulkin da aka yi a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP.

Zanga-zangar na zuwa ne yayin da dakarun da suka kifar da gwamnatin farar hula, suke kokarin ci gaba da damke madafun iko.

Gangamin har ila yau na zuwa ne yayin da kasar ta Nijar take cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai daga Faransa.

Rahotanni sun ce an ji jama’ar da suka taru a wajen zanga-zangar suna furta kalaman nuna goyon baya ga kasashe makwabta da sojoji suka yi juyin mulki, irinsu Mali da Burkina Faso.

A ranar 26 ga watan Yuli, dakarun da ke tsaron fadar Shugaba Mohamed Bazoum suka tsare shi tare da ayyana kifar da gwamnatinsa.

Masu juyin mulki sun bayyana matsalar tabarbarewar tsaro da rashin iya tafiyar da tattalin arzikin kasa a matsayin dalilansu na yin juyin mulkin.

Kasashen duniya da dama ciki har da Amurka da Faransa hade da ECOWAS, AU da Majalisar Dinkin Duniya, sun yi Allah wadai da matakin.

Hafsoshin sojin kasashen kungiyar ECOWAS na taro na kwanaki uku a Abuja, Najeriya, don lalubo hanyoyin da za a sasanta wannan rikicin siyasa.

A makon da ya gabata kungiyar ta ECOWAS ta ba sojojin da suka yi juyin mulki wa’adin kwanaki bakwai su mika shugabancin ga farar hula, tana mai nuni da cewa za ta iya daukan matakin soji idan har suka bijirewa umurninta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG