Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sun Ce Ba Gudu, Ba Ja Da Baya


Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

Jagoran sojojin da suka yi juyin mulki ya yi wannan ikirarin ne a wani lokacin da ake jiran zuwan tawagar ECOWAS/CEDEAO karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar domin samo bakin zaren wannan rikici cikin ruwan sanyi.

NIAMEY, NIGER -Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun yi watsi da matakan da kungiyar ECOWAS ta dauka a zaman da ta yi an Abuja a karshen makon jiya, suna masu cewa babu wata barazanar da za ta sa su ja da baya a manufofin da suka sa gaba.

Shugaban Majalisar CNSP ta sojojin da suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum, Janar Abdourahamane Tchiani ne ya bayyana haka a jawabin da ya yi wa al’ummar kasar ta kafar talbijan a albarkacin zagayowar ranar samun ‘yancin kai ta 3 ga watan Agusta.

Matakin dakatar da tallafin manyan kasashen duniya na daga cikin jerin abubuwan da Janar Tchiani ya tabo a wannan jawabi.

“Mun yi mamaki yadda wadanan kasashe aminnai suka yi hamzarin yin tur da juyin mulki da majalissar CNSP ta jagoranta har ma suka fara hukunta Nijar da al’ummarta tare da dakatar da huldar da ta shafi ayyukan da suke gudanarwa a fannin tsaro.” Ya ce.

Ya kara da cewa su kuwa CEDEAO da UEMOA cikin yanayin daurin kai ne ‘yan Nijer suka sami labarin sun kakaba wa kasar takunkumin irin na rashin imani da rashin adalci da saba doka.

Asali ma a tarihin wata kungiyar kasa da kasa ba a taba daukan irin wannan mataki kan wata kasa ba, karon farko kenan da irin haka ke faruwa ba tare da tuntuba ba, har ma da yi wa kasar Nijar kamuwar kudadenta a bankuna tare da barazanar amfani da karfin soja.

Ya kara da cewa, Majalisar CNSP ta yi watsi da wadanan jerin takunkumi kuma ba wata barazanar da za ta sa ta ja da baya ba daga matsayinta.

Jagoran na Majalisar sojojin da suka yi juyin mulki na wannan ikirarin ne a wani lokacin da ake jiran zuwan tawagar ECOWAS/CEDEAO a karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar domin samo bakin zaren wannan rikici cikin ruwan sanyi.

Kungiyar alkalai ta kasa wato SAMAN a sanarwar da ta aika wa manema labarai dauke da sa hannun sakatarenta mai shara’a Doubou Yahaya ta yi tur da amfani da karfi wajen karbar madahun iko domin a cewarta hanya ce da ta saba wa doka saboda haka ta gargadi sojojin CNSP su gaggauta bin hanyoyin mayar da al’amuran mulki a hannun farar hula.

Amurka a na ta bangare ta bayyana shirin kwashe wasu daga cikin jami’anta da ke Nijar sakamakon lura da yadda abubuwa suka fara canza salo.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sun Ce Ba Gudu, Ba Ja Da Baya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG