Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Na Shirin Fara Karbar Bayanan Da Ake Ba Shugaban Kasa a Kullum


Zababben Shugaban Amurka Joe Biden.

Wannan na zuwa ne yayin da Joe Biden ya damka wa mata sashen sadarwar fadar White House

Ranar Litinin 30 ga watan Nuwamba zababben Shugaban Amurka Joe Biden zai fara karbar bayanan da ake bai wa shugaban kasa a kullum, abin da zai ba shi damar samun rahotannin da hukumomin tattara bayanan sirri ke shiryawa kan batutuwan da suka shafi tsaron kasa yayin da ya ke shirin kama aiki a watan Janairu.

Hakazalika a ranar Litinin din ake sa ran Biden da zababbiyar mataimakiyarsa Kamala Harris za su bayyana sunayen mutanen da za su rike manyan mukamai a fannin tattalin arzikin kasar a gwammatinsu.

Kafofin watsa labarai da dama, bisa ga bayanai daga mutanen da ke da masaniya game da tsarin, sun ba da rahoton cewa, Neera Tanden ita ce za ta jagoranci ofishin kasafin kudi a fadar White House, tare da masaniyar tattalin arziki Cecilia Rouse wacce za ta zama shugabar majalisar masu ba da shawara kan tattalin arziki.

Ranar Lahadi 29 ga watan Nuwamba ne Shugaban mai jiran gado da mataimakiyarsa suka sanar da sunayen matan da aka danka wa sashen sadarwar fadar White House.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG