Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Tattauna Da Takwarorin Sa Na Birtaniya, Canada, Mexico Ta Waya


Shugaba Biden
Shugaba Biden

Firai ministan Birtaniya Boris Johnson ya fadawa shugaba Joe Biden cewa, a shirye yake ya bude sabon babi a yarjejeniyar kasuwancin Amurka da Birtaniya.

Kokarin da Johnson ke yi na neman kulla sabuwar yarjejeniyar kasuwanci ya faro ne daga wata hirar waya tsakanin shugabannin biyu da suka tabo abubuwa da dama a kan matakan da duniya ke dauka na yaki da annobar coronavirus da kuma sanarwar da gwamnatin Biden ta bayar a wannan mako cewa Amurka zata sake shiga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris da kuma komawa hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO, a cewar sanarwa daga fadar firai ministan Birtaiya a Downing Street.

Sabuwar yarjejeniyar ciniki tsakanin manyan kawayen wani babban aiki ne da Johnson ya ba shi muhimmanci fiye da Biden. Birtaniya ta samu cikakken iko a kan shirin kasuwancinta ne a farkon wannan wata, bayan da ta cika sharudan ficewa daga kungiyar tarayyar Turai.

Sakataren jarida a fadar White House Jen Psaki ta fada a ranar Juma’a cewa gwamnatin bata gindaya wani lokaci na kulla sabuwar yarjejeniya ba, yayin da Biden yafi maida hankali a kan yaki da annobar coronavirus da kuma matsawa majalisar dokokin Amurka lamba ta amince da shirin tallafin coronavirus na shugaban kasa na dala triliyan $1.9.

Hirar da Johnson shine akalla na uku da Biden ya yi da takwarorin sa na kasashen waje a ranar Juma’a. Shugaban ya kuma tattauna da firai ministan Canada Justin Trudeau da shugaban kasar Mexico, Andrés Manuel López Obrador da yammacin ranar Juma’a.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG