Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Daukar Matakan Ragewa Amurkawa Radadin COVID-19


Shugaba Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanya hannu a kan wasu dokokin umarnin shugaban kasa hade, da zummar samar da tallafin kudi da na abinci ga iyalai da annobar coronavirus ta yi mummunar tasiri a kan su kana zasu taimakawa ma’aikatan tarayya.

Dokokin zasu kara yawan taimakon abinci, da ci gaba da tallafin da ake baiwa marasa ayyukan yi kana dokokin zasu shirya bada albashi mafi kankanci na dala 15 a duk sa’a guda ga ma’aikatan tarayyar da ‘yan kwantaragi.

"Ya kamata mu dauki mataki yanzu," inji Biden kafin sanya hannu a dokokin umarnin shugaban kasar a fadar White House.

Ya ce Amurkawa da suke ganin ragowa cikin albashin su, suna rayuwar hannu kwarya hannu baka ne, kana ya ce bai yiwuwa mu kyale kuma ba zamu kyale mutanen mu su kasance cikin yunwa ba.

Mutanen da aka kore su daga wuraren aikin su, saboda annoba, yanzu sun samu taimakon abinci.

Biden ya baiwa majalisun kasar shawarar ware kusan dala triliyan biyu domin tallafawa Amurkawa da suke shan wahala daga mummunar tasirin coronavirus, sai dai akwai shakku ko kudurin zai samu goyon bayan ‘yan majalisa a tabbatar da shi.

Majalisar ta tabbatar da kudurin tallafi na dala biliyan 900 a cikin watan Disamba kuma wasu ‘yan majalisa na Republican suna gani babu bukatar karin wani babban tallafi.

Tun da safiyar jiya Juma’a ne darektan hukumar tattalin arziki ta kasa Brian Deese, ya fada a wani taron manema labarai a fadar White House cewa tattalin arzikin kasar na gab da rushewa.

XS
SM
MD
LG