Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bidiyon Wani Ɗan Shekara 10 Da Yake Rera Waka Mai Suna "Beautiful Day" Ya Bi Gari


shafukan sada zumunta
shafukan sada zumunta

Sabon faifan bidiyo da ke daukar hankulan miliyoyin masu amfani da shafukan sada zumunta na wani yaro dan kasar Jamaica mai shekaru 10 yana waka kan kyau da godiya, ya gama duniya.

Wakar, " Beautiful Day," ta samu karbuwa a duk duniya ta hanyar Tik Tok, Instagram da YouTube.

Yayin da bidiyon ya fara yaɗuwa kwanan nan, labarin wakar ya fara ne kusan shekaru goma da suka gabata lokacin da mawaki Jermaine Edwards ya yi wakar mai taken “Beautiful Day” a Jamaica a cikin 2014.

Shekaru da dama bayan haka, Rushawn Ewears dan shekara 10 ya rera wakar a lokacin cin abinci a cikin 2017 a makarantar firamare ta Top Hill a Jamaica. Malaminsa ya yi rikodin sa yayin da ya ke wakar, a lokacin da abokan karatun Ewears ke kallo daga dayan dakin.

An wallafa bidiyon a Facebook, inda aka yi ta rarraba wakar ta hanyar shafukan sada zumunta a duk fadin Jamaica cikin shekaru da suka gabata.

Koda ya ke, sai a 'yan makonnin nan ne bidiyon ya zagaye kasashen duniya tare da makada a duk faɗin duniya su ma su ka sa ke ma wakar fasali.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG