Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Twitter Ya Hana Hada Shafin Da Sauran Abokan Hamayya


Hoton Facebook, da Instagram (AP Photo/Richard Drew, File)
Hoton Facebook, da Instagram (AP Photo/Richard Drew, File)

Kamfanin Twitter ya dakatar da hada dandalin da manyan shafuka irinsu Facebook da Instagram, da abokan hamayyarsa Mastodan, Tribel, Nostr, Post, da Truth Social na tsohon shugaban kasa Donald Trump.

Daga yanzu masu yin amfani da Twitter ba za su iya hada shafin da wasu shafukan sada zumata masu hamayya ba, cikin har da abin da kamfanin ya bayyana a ranar Lahadi da “Shafukan da aka haramta” Facebook, Instagram da Mastodon.

Wannan dai shi ne mataki na baya -bayan nan da sabon mai kamfanin na Twitter Elon Musk ya dauka na dakile wasu kalamai bayan da ya rufe wani shafin Twitter a makon da ya gabata wanda ke bibiyar tafiyar jirginsa na kashin kansa.

“Muna sane cewa da yawa daga cikin masu amfani da mu na yin amfani da wasu shafukan sada zumunta; duk da haka, zuwa nan gaba, Twitter ba za ta bari ayi tallar wasu shafukan sada zumunta ba a Twitter,” in ji kamfanin a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Elon Musk
Elon Musk

Shafukan da aka dakatar sun hada da manyan shafuka irinsu Facebook da Instagram, da abokan hamayyarsa Mastodan, Tribel, Nostr, Post, da Truth Social na tsohon shugaban kasa Donald Trump.

Kamfanin Twitter bai ba da bayanin dalilin da yasa ya hana wadannan shafukan 7 ba, amma ya bar wasu kamar Parler, TikTok ko LinkedIn.

Har ila yau kamfanin Twitter ya hana wasu kamfanoni da suke tallan kafofin sada zumunta da suke hadawa kamar Linktree, da wasu mutane ke amfani suna nuna inda za’a iya samunsu a shafukan yanar gizo daban-daban.

TWITTER-MUSK
TWITTER-MUSK

A baya dai kamfamninm Twitter ya dauki mataki kan daya daga cikin abokan hamayyarsa, Mastodon, bayan da babban shafinsa na Twitter ya wallafa a shafinsa na Twitter game da cece-kuce a kan @ElonJet a makon da ya gabata.

Mastodon ya bunkasa cikin sauri a cikin ‘yan makonnin da suka gabata, a matsayin zabi ga masu amfani da Twitter wadanda ba su jin dadin gyaran da Musk ya yi na Twitter ba, tun lokacin da ya sayi kamfanin a kan dala biliyan $44 a karshen watan Oktoban da ya gabata kuma ya fara maido da shafukan da suka karya dokokin shugabancin Twitter na baya na hana nuna kyama da sauran illoli.

TWITTER MASTODON
TWITTER MASTODON

Wasu masu amfani da Twitter sun hada sabon bayanninsu na shafin Mastodon kuma suna karfafa masu bibiyarsu su same su a can. Yanzu an dakatar da hakan a kan Twitter, kamar yadda suke kokarin kewaye hanin ta hanyar rubuta “Instagram dot com” da sunan mai amfani, maimakon zuwa shafin kai tsaye.

Nan take dai kamfanin Meta mai Instagram da Facebook bai mayar da martani ba da aka tuntubesu a ranar Lahadi.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG