Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Binciken Rasha: Nunes Ya Ajiye Mukaminsa a Matakin Wucin-Gadi


House Intelligence Committee Chairman Rep. Devin Nunes, R-Calif. is pursued by reporters as he arrives for a weekly meeting of the Republican Conference with House Speaker Paul Ryan and the GOP leadership, March 28, 2017, on Capitol Hill in Washington.

Shugaban kwamitin dake kula da hukumomin tattara bayananan sirri a Majalisar dokokin Amurka, Devin Nunes ya sauka daga mukaminsa a mataki na wucin gadi a binciken zargin da ake yi wa Rasha na cewa ta saci bayanan sirrin Amurka gabanin zaben 2016.

Nunes ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, inda ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan da wasu suka gabatar da korafin cewa akwai yiwu war ya saba ka’ida a aikinsa.

Ya kara da cewa kungiyoyin masu rajin sassaucin ra’ayin sun zarge shi da rashin bin ka’idojin da suka danganci da’ar gudanar da aikin majalisar.

Shugaban kwamtin ya ce zai janye har sai an kammala binciken an gano ainihin gaskiyar lamarin.

“Duk da cewa wannan korafin da suka gabatar ba shi da tushe, na yi ammanar cewa zai fi alheri idan na bar abokanan aikina Mike Conaway da Trey Gowdy da kuma Tom Rooney su kula da jagorancin wannan kwamitin dake binciken Rasha na dan wani lokaci.” In ji Nunes.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG