Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Gano Mutumin Da Ya Dasa Bam a Tashar Jirgin St. Petersburg


Kamfani dillacin labaran kasar Rasha ya ce mahukuntan kasar sun ce sun gano wanda ake nema da dasa bam din da ya tashi a tashar jirgin kasar St. Petersburg a jiya littini.

Kamfanin dillacin labaran ya ce ‘yan sandan kasar sun ce, sun yi imanin dan kunar bakin wake ne, dan shekaru 23 da haihuwa daga kasashen tsakiyar Asiya, ya aikata wannan danyen aiki.

Kamfanin dillacin labaran ya ambato ‘yan sandan kasar na cewa wanda ya dana wannan bam din ya na dauke da shi ne cikin jirgin a cikin wani kunshi.

Sai dai kawo yanzu ba wanda ya dauki alhakin aikata wannan aika-aikan, da aka yi a birni na biyu mafi girma a kasar ta Rasha da ya yi dalilin mutuwar mutane 11, kana wasu 50 suka samu rauni iri daban-daban.

Masu binciken abinda aka hada bomb din dashi sun ce sinadarin da aka yi amfani da shi wajen hada bam din ya na da nauyin da zai huda kofar jirgin kasan wanda yake ya na da kaurin gaske.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG