Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biyan Basukan Da Aka Ba Jihohi A Halin Yanzu Matsala Ce-Gwamnan Bauchi


Gov Bala Muh'd
Gov Bala Muh'd

Batun da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi cewa zata fara cire kudaden rancen tallafin da ta bai wa gwamnatocin jihohin kasar domin biyan hakkokin ma’aikata kamarsu albashi da kuma fansho ya fara jefa tunani a zukatan gwamnonin kasar musammam wadanda ba a lokacinsu ba ne aka bada tallafin

Bincike ya nuna cewar jihohin kasar talatin da biyar ne suka karbi wadannan basussuka na kimanin Naira biliyan dari biyu da goma sha hudu in banda jihar Legas, wanda hakan ke nufin cewa jihohin da suka karbi tallafin akalla kowace ana tsammanin za ta biya Naira biliyan goma sha bakwai da miliyan dubu dari biyar.

Wannan yunkurin karbo kudaden ya biyo bayan kafa kwamiti ne da gwamnatin tarayyar kasar ta yi domin bin diddigin yadda gwamnonin suka yi amfani da kudaden tallafin, inda kwamitin ya gano cewa wasu jihohin sun yi amfani da kudaden bisa manufa a yayin da wasu jihohin kuwa su ka yi amfani da kudaden don kashe gararin gabansu.

Gwamnan Bauchi, Senata Bala Muhammed Abdulkadir (Kauran Bauchi) ya bayyana cewa wannan matsala ce.

Sai dai kuma a wani tsokaci masanin tattalin arziki kuma tsohon shugaban kungiyar kwadago kwamred Abdullahi Koli ya ce fara biyan bashin a yanzu zai maida hannun agogo baya musamman ga batun biyan albashi a jihohi.

Ga dai rahoton Abdulwahab Mohammed a kan wannan batu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG