Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Jefa Kuri'a Kan Shirin Lafiya Ya Shiga Rudu A Majalisar Amurka


Mitch McConnel

Majalisar Dattawan Amurka zata jinkirta batun kada kuri'a akan tsarin kiwon lafiyar Republican.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawan Amurka Mitch McConnel, ya ce zai jingirta shirin kada kuri'a kan Dokar Tsarin lafiya ta Republican.

Sanarwar ta McConnel ta biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa likitoci sun shawarci Sanata John McCain da ya cigaba da zama a Arizona na tsawon sati guda, bayan wata tiyatar da aka masa jiya Asabar, inda aka cire masa wani daskararren jini a saman idonsa na hagu.

"Da Elaine da ni, da ma dukkannin 'ya'uwa na Majalisar Dattawa, na fatan alheri ma John da kuma fatan waraka cikin gaggawa," a cewar McConnel a wata takardar sanarwa. Ya kara da cewa, "A yayin da John ke murmurewa, Majalisar za ta cigaba da gudanar da wasu ayyukan Majalisar.

Rashin McCain a Majalisar da ke fama da rarrabuwar kawuna ya jefa batun jefa kuri'a kan shirin lafiyar cikin rudu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG