Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cibiyar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Amurka Za Ta Taimakawa Najeriya


Taron Cibiyar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Amurka a Najeriya

A daidai lokacin da ake neman bakin zaren magance matsalolin tashe-tashen hankula da rikicin Boko Haram, yanzu cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Amurka da ake kira ‘US Institute of Peace’ ta isa Najeriya tare alkawarin taimakawa don magance matsalar.

A ziyarar da shugabanin cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Amurka suka kai Najeriya, sun gana da masu ruwa da tsaki tare da nuna wani majigin ta’addancin Boko Haram a Najeriya, majigin da Muryar Amurka ta shirya tare da gudunmawar wasu cibiyoyi.

Tun farko a jawabinta na maraba Dakta Dawn Dekle, shugabar jami’ar Amurka dake Najeriya, ta yaba da wannan yunkuri da cibiyar ta Amurka keyi, wajen magance tashe-tashen hankulan dake faruwa a wasu kasashe.

A nata jawabin shugabar cibiyar Nancy Limborg, ta ce manufar ziyararsu ita ce ilimantarwa da kuma zaburar da al’umma musamman masu ruwa da tsaki game illoli da kuma sanin matakan yaki da ayyukan ta’addanci, kamar yadda cibiyar ta taimaka a wasu kasashen duniya.

Haka kuma ta yaba da irin gudumawar da wasu ‘yan aikin sakai suka bayar irin Sarauniyar Maharba, Aisha Bakari Gombi, macen da ta taimaka a yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram.

To sai dai kuma ziyarar tasu ta zo ne yayin da ‘yan Majalisar wakilai a Najeriya ke kiran da a kafa barikin Sojoji a yankin Mubi, da a baya ta zama tungar ‘yan Boko Haram a arewacin jihar Adamawa.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG