Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Sun Kashe Sun Kuma Sace Ma'aikatan Kiwon Lafiya A Rann, Borno


Dr Kachi, likita na bakwai da mayakan Boko Haram suka kashe a Rann, Borno
Dr Kachi, likita na bakwai da mayakan Boko Haram suka kashe a Rann, Borno

A cewar shugaban wata kungiyar kiwon lafiya dake taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita a yankin Rann, rage jami'an tsaro ya ba 'yan Boko Haram damar kewaye barikin soji dake garin inda suka fatattakesu suka kashe wasu har da wani likita tare da sace wasu mata ma'aikatan kiwon lafiya

Mayakan Boko Haram sun kai wani wawan hari a sansanin sojojin Najeriya dake garin Rann cikin jihar Borno.

'Yan Boko Haram din sun fatattaki sojojin suka kashe na kashewa kana suka sace wasu ma'aikatan kiwon lafiya dake aiki a cibiyar Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban gidauniyar Smile Medical Care Foundation dake tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, Dr. Sale Abba ya yiwa Muryar Amurka karin bayani.

A cewarsa ba zato ba tsammani aka rage jami'an tsaro sai da yamma aka fara jin harbe harbe a cikin barikin sojojin dake garin. Ya ce sojojin basu ankara ba kawai kwatsam sai suka ji ana yaren Kanuri. Daga nan sojojin suka sani mayakan Boko Haram sun kewaye barikinsu.

Inji Dr. Abba da lamarin ya fi karfin sojojin sai suka gudu zuwa cikin jeji. A cikin haka ne aka kashe mutane uku kuma daya daga cikinsu shi ne Dr. Kachi. Shi ne likita na bakwai da kungiyar Boko Haram ta kashe a yankin. Baicin kashe shi Dr. Kachi 'yan Boko Haram din sun sace wasu masu jinya, wato nurses guda uku, Hauwa Mohammed da Safina da Halima Muhammad wadda ta buga waya a daidai lokacin da 'yan Boko Haram din ke kokarin saceta.

Safina, daya daga cikin Nurses da mayakan Boko Haram suka sace a Rann
Safina, daya daga cikin Nurses da mayakan Boko Haram suka sace a Rann

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin kakakin sojojin Birgediya Janar Chukwu amma ba ta ci nasara ba.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG