Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Zai Kai Ziyarar Jaje a Dapchi Da Wasu Jihohi


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara yankunan da suka yi fama da rikice-rikice a 'yan kwanakin nan ciki har da jihar Benue da Yobe da Zamfara da Taraba da kuma Rivers inda aka yi asarar rayuka da dama da kuma dukiyoyi.

Fadar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce shugaban zai kai ziyara jihohin Benue da Yobe da Zamfara da Taraba da kuma Rivers, wadanda suka yi fama da tashe-tashen hankula a ‘yan kwanakin nan.

Fadar ta Shugaban Najeriya ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter.

“Bayan da muka yi nazari kan rahoton da aka gabatar mana, shugaban ya yanke shawarar zai kai ziyarar ganewa idonsa kan batutuwan da suka faru, domin ya hadu ya kuma jajantawa al’umomin da abin ya shafa.” Sakon Twitter ya ce.

Sakon ya kuma kara daga cewa “daga yau 5 ga watan Maris, zai ziyarci Taraba, Benue, Yobe, Zamfara da kuma Jihar Rivers.”

Buhari ya sha suka kan kin kai ziyara wadannan yankuna da aka rasa rayuka da dumbin dukiyoyi, musamman a jihar Benue da rikicin makiyaya da manoma ya haddasa mutuwar mutane dama a bara.

A karshen makon nan, ;'yan najeriya a kafafen sada zumunta na zamani, sun yi ca akan shugaban, bayan da ya halarci bikin ‘yar gwamnan Kano, kasa da makwanni biyu da ‘yan Boko Haram suka sace ‘yan matan makarantar Dapchi 110 a jihar Yobe.

Masu lura da al’amura dama na ganin kamata ya yi a ce shugaban ya kai ziyara yankin na Dapchi.

Ita ma jihar Taraba, wacce ko a karshen a makon an tafka rikici, ta sha fama da rikice-rikicen makiyaya da manoma.

A jihar Zamfara da ‘yan fashi suka addaba, mutane da dama sun mutu a ‘yan kwanakin nan a kauyen Birane, bayan da wasu ‘yan bindiga suka far ma kauyen.

A jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, wasu ‘yan bindiga sun kai hare-hare, ciki har da wanda aka kai a wata mujami’a inda aka kashe masu ibada.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG