Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kai Hari A Kan Sojojin Najeriya A Kusa Da Maiduguri


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

A yammacin jiya Litinin da misalin karfe shida ne wasu da ake zaton 'yan boko haram ne suka kai hari a kan jami’an soja a kwauyen Auno dake daf da shiga garin Maiduguri.

Wannan harn dai yasa mazauna wannan kauyukan arcewa daga gidajensu zuwa cikin daji dan gudun abin da zai kai ya komo, yayinda aka ce jami'an sojan sun yiwa mahara ba dadi, inda aka ce sun yi shigar burtu irin na sojan suka kuma soma buda wuta kan jami'an sojan, suma jami'an sojan sun maida masu da martani suka kuma ci galaba a kan maharan.

Haka zalika wannan harin ya rutsa da wasu matafiya dake bin wannan hanyar kamar wani da wannan hari ya rutsa da shi a kan hanyarsa na dawowa daga sayan icce a garin na Auno ya yiwa wakilin Muryar Amurka bayani ta wayar tarho. Mutumin yace yanzu haka kowa na ta kansa ne ya tsira da rayuwarsa.

Wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda ya ci gaba da tattaunawa da wasu da suka arce suka buya a ciki daji bayan wasu sun fada masa bindiga ta kama wani kuma tuni an kai shi asibiti. Wani da ya gudu da ransa ya shaida mana cewa maharan da sojojin sun yi bata kashi kuma haka ne ya yi sanadiyar mazauna kauyen suka shiga daji.

Wannan lamari yana aukuwa ne a daidai lokacin da wani kwamiti mai karfin gaske karkshin jagorancin gwamnan jihar Borno Ukasha Shattima uka aikawa shugaba Muhammadu Buhari rahoto a kan halin da ake ciki game da tsaron jihar Borno.

Ga rahoton da Haruna Dauda ya aiko mana daga Maiduguri:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG