Accessibility links

Bom Ya Fashe A Kusa Da Gidan Sarkin Kano


Kofar mai Martaba Sarkin Kano, Ado Bayero, a lokacin zaben da ya shige.

Wani abu mai kama da bom ya fashe a kusa da gidan Sarkin Kano, a yammacin jiya Laraba.

WASHINGTON, D.C - Wasu mutane guda biyu sun tuka babur mai kafafu uku, wanda aka fi sani da adai-daita sahu misalin karfe 8 na dare, inda suka tayar da abun fashewar.

Ma’aikaciyar Sashen Hausa na Muryar Amurka, Halima Djimrao ta tattauna da wani wanda ya ga abunda ya faru, Baffa Mukhtar Kwaru inda ya bayanna mata cewa mutane sun kashe daya daga cikin wadanda suka tabuka wannan lamari, sannan an kama abokin aikinsa:


Wannan shine karo na biyu na irin wannan tashin hankali yake kusantar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero a watanni 4 kennan da suka wuce.

A karshen watan Junairu ne, wasu ‘yan bindiga suka kai wa jerin gwanon motocin Sarkin Kanon hari a kusa da Masallacin Murtala dake birnin Kano, inda mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata a ciki harda mutane dake kusa da Sarkin.
XS
SM
MD
LG