Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom Ya Tashi A Mota a Birnin Mogadishu Dake Kasar Somaliya


Mutane shidda ne suka rasa rayukansu sakamakon harin bom na mota da aka kai a kasar Somaliya.

Jami’an tsaro guda biyar da kuma wani masanin hako ma’adanai sun mutu a yayin da suke kokarin warware wani bom da aka boye cikin mota a yau Laraba a babban birnin Somaliya.

Mai Magana da yawun rundunar 'yan sanda Mohamed Yusuf Omar yace an ajiye motar ne a kusa da ofshin yan sanda a Unguwar Wadajir dake Mogadishu.

Madale ya fadawa Sashen VOA na Somaliya “Jami’an tsaro sun zargi direban motar inda suka tsare shi suka kuma yi kokarin cire bom din amma ya tashi,”

Ya kara da cewa da’alamar bom din an tada shi ne da naura daga nesa.

Har ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma ana zargin wannan irin ayyukan da kungiyar Al-shabab ke yi ne.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG