Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom ya Tashi Bayan Rufe Tafsirin Sheikh Dahiru Usman Bauchi


Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Wani bam ya tashi a daidai lokacin da jerin motocin Sheikh Dahiru Usman Bauchi ke wucewa a bayan rufe tafsirin azumin Ramadan a garin Kaduna.

Rahotanni sun ce mutane da dama sun mutu, kuma har gilashin motar shaihin malamin ya farfashe, amma kuma babu abinda ya same shi.

Wannan shi ne karo na biyu da ake kai harin bam a kusa da inda wannan shaihin malami yake.

XS
SM
MD
LG