Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsige Gwamnan Adamawa Ya Bar Kura Baya


Murtala Nyako, gwamnan Jihar Adamawa da aka tsige daga mukaminsa.

Biyo bayan tsige gwamnan Adamawa Murtala Nyako da kuma ajiye mukami da aka ce mataimakin gwamnan yayi yanzu haka wani rikici ya sake kunno kai a cikin jihar.

Wasu kusoshin PDP sun ki amincewa da batun tsayawar wasu da suka koma jam'iyyar takarar kujerar gwamnan jihar.

Cikin wadanda suka koma jam'iyyar PDP kuma suna kokarin tsayawa takarar kujerar gwamna har da tsohon gwamnan soja a jihohin Borno da Legas Janaral Buba Marwa. A wani taron PDP Buba Marwa ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan a zaben cike gurbi da za'a yi.

Tun farko a cikin jawabinsa mataimakin shugaban PDP a jihar Adamawa ta tsakiya Alhaji Danjuma Iliyasu yace a wannan karon ba zasu amince da nadin Abuja ba. Haka ma wasu 'yan takarar jam'iyyar irin su Dr Umar Ardo suka ce ba zasu amince da wadanda suka kira sabbin komowa ba domin tsarin mulkin jam'iyyar ya hana. Sabili da haka ta yaya Janaral Buba Marwa zai iya tsayawa takarar kujerar gwamna a karkashin PDP yanzu bayan ya fice daga jam'iyyar kafin ya sake dawowa kwana kwanan nan.

Yanzu ma wasu suna kiran mukaddashin gwamnan shi ma ya fito ya nemi kujerar tunda doka bata hanashi ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG