Wani Kakakin gwamnatin yankin, Attaullah Khogyani, ya gayawa VOA cewa limamin masallacin na daga cikin wadanda suka mutu a Masallacin wanda ke Gundumar Rodat.
Hukumomin sun ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya karu saboda mutane da dama sun ji munanan raunuka.
Wannan yanki ya kasance wuri ne da ke dauke da mayakan kungiyar IS da na Taliban da suka yi kaura daga Pakistan.
A daya banagren kuma, wani Kakakin ma’aikatar cikin gidan kasar ta Afghanistan, Sediq Seddiqi, ya tabbatarwa Muryar Amurka cewa an yi garkuwa da wata Ba’indiya da ke aiki da wata kungiyar ba da agaji a Kabul.
Judith D’Souza, mai shekaru 40, tana aiki ne da wata gidauniya mai suna Aga Khan Foundation.