Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boma-bomai Sun Fashe a Maiduguri


Mutane sunyi dafifi kewaye da inda boma-boman ya tashi a Maiduguri.

Da Azahar ne Talatannan wasu boma-bomai da aka hada a cikin motoci uku suka fashe a unguwar Mulai dake birnin Maiduguri.

Rahotanni na nuna cewa motoci hudu ne masu kirar Golf aka shiryasu da boma-bomai, amma uku ne kawa suka fashe.

Bayanen da muke da su yanzu na nuna cewa a kalla mutum daya ne ya rasa ransa, kuma masu gani da ido, sunce wani mutum a daya daga cikin motocin ya fito yayi harbin mai kan uwa da wabi.

Kwamishin 'yan Sandan jihar Gambo Lawal ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai bai bada karin bayani ba.

Birnin Maiduguri itace tungar 'yan bindigannan masu tayar da kayar baya da aka fi sani da Boko Haram.

Zamu kawo muku karin bayani.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG