Accessibility links

Mazauna Maiduguri Suna Kokawa Kan Mawuyacin Halin Rayuka da Suka Shiga

  • Aliyu Imam

Sojan Najeriya cikin motar yaki.

Mazauna Maiduguri fadar jihar Barno sun koka kan mawuyacin halin rayuwa da suka fada, saboda yadda matsalolin tsaro suka takura komi.

Wannan baiwar Allah wacce ta nemi woyar Sashen Hausa domin ta bayyanawa duniya hali d aake ciki a Maiduguri ta zanta ne da Aliyu Mustapahn sokoto, ta bayyana cewa magidanta walau ma’aikatan gwamnati ko ‘yan kasuwa zasu fita su wuni su dawo hanu banza, domin babu abunda yake tafiya komi ya tsaya cik.

Malama Fatsuma tace ita kanta tana godewa Allah amma a gaskiya makwabta suna cikin halin- kaka-nika-yi. Tace ma’aikatan gwamnati ko masu sana’ar hanu duk babu abunda yake tafiya.

Da aka gaya mata cewa ai sanannen abu ne ga kowa hali da mutanen Barno da Yobe da sauransu suke ciki, sai ta ce ai na Maiduguri yafi tsanani fiyeda ko wani wuri. Tace sai magidanci ya fita tunda da safe ya taka da kafa zuwa unguwa kamar Bulumkutu ya bar mata da yara, ya dawo hannu banza.

Da aka tambayeta shin ana bude kasuwanni, kuma ina matsalar take ne ana fuskantar karancin kayayyaki ne kodai akwai kaya masu saye ne babu? Sai malama Fatsuma tace ai akwai kayayyaki masu saye ne babu, saboda babu kudi.

Malama Fatsuma tace galibin masu hali sun kwshe iyalansu sun bar Maiduguri. Daga nan tayi kira ga masu hali da hukuma su tallafwa jama’a domin saukaka hali d a suke ciki.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG