Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BORNO: Sama Da Mayakan ISWAP 104 Da ‘Yan Uwansu Sun Mika Wuya


Wasu mayakan Boko ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)
Wasu mayakan Boko ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)

Akalla mayakan kungiyar ISWAP 104 na lardin Yammacin Afirka, sun mika wuya ga sojojin Najeriya a jihar Borno.

Hedikwatar rundunar sojin Najeriya ta bayyana hakan ne yau Litinin ta wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

A cewar sanarwar, wadanda suka mika wuya ga rundunar ta 25 Task Force Brigade Damboa sun hada da maza 22, mata 27 da yara 55.

Sanarwar ta ce, "ISWAP da iyalansu da adadin su ya kai 104, da suka hada da maza 22, mata 27 da yara 55 sun mika wuya ga dakarun ta 25 Task Force Brigade Damboa, jihar Borno a ranar Asabar 5 ga Fabrairu 2022."

Rahotanin na cewa iyalan ‘yan ta’addar ISWAP na ficewa daga Marte sakamakon mumunar farmakin da sojoji suka kai musu.

XS
SM
MD
LG