Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buffon Zai Bar Juventus A Karshen Kakar Wasa Ta Bana


Gianluigi Buffon (Juventus)
Gianluigi Buffon (Juventus)

Sai dai ya ce mai yiwuwa, zai koma wata kungiyar idan har ya samu tayin da ya kwanta masa a rai.

Mai tsaron ragar kungiyar Juventus a gasar Serie A ta Italiya, Gianluigi Buffon, ya ce zai bar kungiyar idan kwangilarsa ta kare a karshen kakar wasa ta bana.

Sai dai ya ce mai yiwuwa zai koma wata kungiyar idan har ya samu tayin da ya kwanta masa a rai kamar yadda shafin yanar gizon Sky Sports ya ruwaito.

Dan shekara 43, Buffon ya je kungiyar ta Juventus ne a shekarar 2001 kuma tuntuni yake zaune a wurin.

Ko da yake, ya yi kakar wasa daya da kungiyar Paris Saint Germain ta PSG a tsakanin 2018-2019.

Ana yi wa Buffon kallon daya daga cikin masu tsaron raga da suka yi fice a duniya a wannan zamani.

Sannan da shi Italiya ta lashe kofin gasar kofin duniya ta FIFA a shekarar 2006.

Ya taba lashe gasar Serie A sau goma da kuma kofin gasar Coppa Italia tare da kungiyar ta Juventus.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG