Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hushpuppi: An Maye Gurbin Abba Kyari Da Tunji Disu


DCP Tunji Disu (Hoto: Channels TV)
DCP Tunji Disu (Hoto: Channels TV)

Kafin nadin nasa a matsayin sabon kwamandan wannan runduna ta musamman, Disu ya yi aiki a matsayin kwamandan rundunar aiki da cikawa ta RRS a Lagos.

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya nada mataimakin kwamishinan 'yan sanda Tunji Disu a matsayin sabon kwamandan rundunar 'yan sanda ta musamman dake yaki da manyan laifuka a kasar, wato Inteligence Response Team ko kuma IRT a takaice.

Shi dai DCP Tunji Disu zai maye gurbin DCP Abba kyari ne da aka dakatar biyo bayan zargin rashawa da ake masa.

Sufeto Janar din ya nemi sabon kwamandan da ya yi aiki bisa kwarewa da kuma nuna sanin yakamata.

Kafin nadin nasa a matsayin sabon kwamandan wannan runduna ta musamman, Disu ya yi aiki a matsayin kwamandan rundunar aiki da cikawa ta RRS a Lagos.

Sannan ya yi mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai lura da aikace-aikace a hedkwatar 'yan sandan kasar, kazalika ya taba zama kwamandan tawagar 'yan sandan Najeriya da su ka yi aikin samar da zaman lafiya a yankin Dafur na kasar Sudan.

DCP Tunji wanda yake da takardun shaida har digiri biyu ya halarci kwasa- kwasai a ciki da wajen Najeriya ciki har da Burtaniya da Botswana.

A ranar Lahadi aka dakatar da Kyari daga wannan mukami biyo bayan bincike da aka kaddamar kan tuhumar da wata kotun Amurka take masa na hannu a wata badakala ta cin hanci da ta shafi Abbas Ramon, wani dan Najeriya da ke fuskantar shari'a a Amurka.

Ana zargin Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi da laifukan damfara ta yanar gizo da kuma halalta kudaden haram.

Yayin binciken Hushpuppi an gano cewa Kyari ya taba karbar cin hanci a wajen Hushpuppi, zargin da Kyarin ya musanta.

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG