Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Na Kokarin Ya Kama Ni – Obasanjo


Shugaba Buhari da Obasanjo
Shugaba Buhari da Obasanjo

Takaddamar da ke tsakanin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, ta dauki sabon salo, bayan da Obasanjon ya yi zargin cewa gwamnatin na shirye-shiryen kama shi, zargin da gwamnatin ta Buhari ta musanta.

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da kitsa shirye-shiryen kama shi.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai yada labaransa, Kehinde Akinyemi, kamar yadda kusan daukacin jaridun Najeriya suka wallafa.

A cikin sanarwar, Obasanjo ya ce ana shirin a kama shi ne saboda yana sukar gwamnatin ta Buhari.

A watan Janairu tsohon shugaba Obasanjo ya fitar da wata wasika yana sukan gwamnatin Buhari, yana mai cewa gwamnatin ba ta tabuka komai ba.

Wasikar ta Obasanjo har ila yau ta shawarci shugaba Buhari da kada ya sake tsayawa takara a zaben 2019.

Sanarwar ta Obasanjo ta ce ta gano cewa ana kulle-kullen saka sunansa a jerin sunayen mutanen da ake so a kashe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Ta kuma kara da cewa, ana so a yi amfani da hukumar EFCC domin a kama shi.

A kwanakin baya, shugaba Buhari ya fito ya zargi Obasanjo da barnatar da dala biliyan 16 wajen ayyukan samar da wutar lantarki, amma har ya sauka wutar ba ta samu ba.

Sai dai Obasanjo a cikin sanarwar, ya ce ba zai daina tsokacin da yake yi wajen ganin ya kare hakkin ‘yan Najeriya ba.

Da Ma Mai Kaza a Aljihu Ba ya Jimirin "Ass" – Lai Mohammed

A mataki na martani, Ministan yada labaran gwamnatin ta Buhari, Lai Mohammed, ya ce kalaman na Obasanjo, wata dabara ce ta dauke hankalin gwamnatinsu wajen mayar da hankalin da ta yi kan gudanar da ayyukan jama’a.

Lai ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a a Legas, kamar yadda jaridar Premium Times da Daily Trust suka wallafa.

Ya kuma kara da cewa “wadanda ke da kaza a aljihu suke jimirin ass,” yana mai musanta zargin cewa ana so a lankayawa Obasanjon wani sharri.

Da Ma Mun Fada - PDP

Ita ma babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta fito ta bayyana kaduwarta kan kalaman na Obasanjo, inda ta ce zargin nasa ya jaddada matsayarsu ta cewa gwamntin ta Buhari tana farwa bangaren ‘yan adawa da ke kalubalantar ta.

PDP ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan ya sa hannu kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG