Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Jajantawa Niger Kan Rasuwar Ministan Kwadagon Kasar


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajantawa shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou ta wayar tarho game da rasuwar Ministan Kwadago, Mohammed Ben Omar.

Shugaba Buhari ya kuma mika sakon ta’aziyya ga gwamnati da kuma iyalan mamacin tare da daukacin al’ummar Nijer bisa ga wannan rashin da suka yi.

Shugaban ya bayyana marigayi minista, wanda ya kasance kakakin gwamnatin Nijer a karkashin Shugaba Mamadou Tandja, sannan kuma ya yi aiki a majalisar, a matsayin gogaggen dan siyasa da ya sadaukar da komai, don wadata da ci gaban tattalin arzikin kasar.

Shugaban kasa yayi addu'ar Allah Madaukakin Sarki ya baiwa dangin marigayi Ministan dangana, da kuma ya ba marigayin dawwaman hutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG