Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Kammala Ziyarar Yakin Neman Zabe A Jihar Kano


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Dazu da maraice shugaban Najeriya ya kammala ziyarar yakin neman zabe a Kano, sai dai shugaban bai yi wani sabon alkawari ba musamman ta fuskar lamuran da suka shafi farfado da masana'antun Kano da harkokin kasuwanci.

Gabanin bayyana a dadalin taron, sai da shugaban ya bude wata gada da gwamnatin Kano ta gina a daf da Barikin sojoji na Bokavo kuma ya kai ziyarar neman tabarraki fadar mai martaba sarkin Kano Malam Muhamamdu Sanusi na biyu.

Dubbun dubatun mutane ne suka yi dafifi domin tarbar shugaban, sai dai a iya cewa taron ya saba da wadda aka saba gani a lokutan baya, inda Kano kan tsaya cik har sai shugaban ya kammala ziyara.

A wannan karon jama'a da dama musamman a sassa daban daban na birnin Kano sun ci gaba da harkokin su.

Domin karin Bayani saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG