Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Taya Kristoci Murnar Bikin Kirsimeti


Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Kristoci murnar bikin Kirsimeti da tare da fatan shiga sabuwar shekara lafiya.

A wani sakon gaisuwar Kirsimeti da ya aikawa 'yan Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari, ya sha alwashin yin aiki tukuru don ci gaban talakan kasar.

"Ina tabbatar wa ‘yan uwana cewa wannan gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen ganin an daukaka darajar rayuwar talakawan Najeriya."

Haka kuma ya yi kira ga 'yan dukkan 'yan Najeriya da suje ayi musu allurar rigakafin Coronavirus, ganin yadda a wannan lokacin rigakafin ke kare mutane tare da hana yaduwar cutar.

Cikin sakon, ya tabo batutuwa masu yawa ciki har da na tsaro, inda ya tabbarwa 'yan Najeriya irin nasarorin da jami'an tsaron kasar suke samu, duk kuwa da wasu kalubale da har yanzu ake fama da su.

Shugaban ya kuma ce ya tattauna batun kara kaimi ga yakin da matsalar tsaro a yankin Yammacin Afirka da takwarorinsa na kungiyar ECOWAS.

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG