Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Taya Ruto Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Kenya


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Hoto: Facebook/Fadar shugaban kasa)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Hoto: Facebook/Fadar shugaban kasa)

Bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Kenya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya William Ruto, murnar lashe zaben.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakinsa Femi Adesina, shugaba Buhari ya yabawa al’ummar Kenya bisa yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, wanda ya sake nuna cewa tsarin dimokuradiyya, dabi'u da ka'idoji sun kasance hanya mafi kyau da jama'a za su zabi shugabanninsu da kuma dora su a kan su.

Shugaba Buhari ya ce Najeriya na mutunta kasar Kenya a matsayin babbar abokiyar kawance wajen yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, wanda dogon tarihi na abotar tattalin arziki da cinikayya, da hadin gwiwa mai inganci da kungiyoyin kasa da kasa kamar kungiyar Tarayyar Afirka, da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashe masu tasowa.

Tun farko dai, shugaban hukumar zabe na kasar Kenya ya bayyana mataimakin shugaban kasar William Ruto, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa mai tsauri - amma wasu jami'an zabe hudu sun yi watsi da sakamakon, lamarin da ya haifar da shakku da rudani kan sakamakon.

A ranar Litinin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kenya, ya ce Ruto ne ya lashe zaben zagayen farko da kashi 50.49 na kuri’un da aka kada, wanda ke gaban tsohon firaminista Raila Odinga da kashi 1.5 cikin dari.

Sai dai 'yan mintoci kafin Wafula Chebukati ya sanar da sakamakon, mataimakiyar shugabar hukumar zaben Juliana Cherea ta ce ita da wasu kwamishinonin uku "ba su amince da sakamakon zaben."

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, kakakin babban abokin hamayyar Ruto, Raila Odinga, ya yi watsi da sanarwar da shugaban hukumar zaben ya yi a matsayin Ruto ne ya yi nasara.

A duk lokacin da ake gudanar da tantancewar da aka fara a ranar Laraba, an yi ta zargin magudin zabe da kuma yadda jami'an zabe ke tafka magudi, musamman daga bangaren Odinga.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG