Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yabawa Manoma Kan Yadda Tsarin Da Gwamnati Ta Samar Yake Kyakkyawan Tasiri


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Hoto: Fadar shugaban kasa)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma’a a garin Daura na jihar Katsina, ya yabawa manoman kasar kan yadda suke noman shinkafa da sauran kayan masarufi, inda ya bayyana jin dadinsa kan yadda manufofin noma na gwamnati ke aiki yadda ya kamata.

Shugaban ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai daban-daban da suka hada da rufe iyakokin kasa har na tsawon shekaru biyu domin amfanin manoma wadanda su ne ginshikin tattalin arzikin yankunan karkara, inda ya nuna farin cikinsa da cewa wadannan ayyuka sun yi wa al’umma aiki mai kyau.

Da yake zantawa da zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar Katsina a ziyarar da suka kai masa na bikin Sallah, shugaba Buhari ya ce “Ina da kyakkyawar fahimtar kasar nan da al’ummarta. Shi ya sa muka kafa wadannan manufofin noma. Na ce dole ne mu shuka abin da muke ci kuma mu ci abin da muke nomewa.

Wannan kasa ce da ta taba dogaro da shinkafar waje. Mun rufe iyakar shigowa da shinkafar waje. Na ce me ya sa ba za mu iya cin shinkafar Najeriya ba, kuma da tsare-tsaren da aka yi, yanzu ‘yan Nijeriya suna cin shinkafar gida.”

“Na sami wani mutum mai karfin zuciya (Hamid Ali) da zai iya yin aiki a Hukumar Kwastam. Watarana ya zo wurina yana cewa sun tare tankokin mai guda 20 suna shirin tsallakawa kan iyaka. Na ce masa ya sayar da man fetur da tankokin yaki ya sa kudin asusun gwamnati na TSA. A da, da wannan kuɗin ya bace ya shiga aljuhun wasu da sunan asusun 'gwamnati' "

Alhaji Ya’u Umar Gojo-Gojo, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu ya yabawa shugaban kasar bisa bullo da wasu matakai na kawo sauyi a harkar noma domin kara samun kudin shigar manoma a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Kwamishinan ya kuma yi wa shugaban kasa karin haske kan yanayin tsaro a jihar, inda ya ce dokar da aka yi wa gyaran fuska ta jihar ta saka kowa a cikin sha'anin gwamnatin jihar da ta kananan hukumomi da sarakunan gargajiya da kuma talakawan kasa inda kowannensu yake bayar da tasa gudunmuwar wajen ganin an rage barazanar tsaro da jihar ke fuskanta.

Shugaba Buhari ya sake nanata kalaman da ya yi tun farko cewa gonar Daura da ya gada daga magabatansa ita ce abu na gaba dake zuciyarsa idan ya bar mulki a shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG