Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Da Aka Kai Jihar Kaduna


Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)

A karshen makon da ya gabata, wasu 'yan bindiga suka kai hare-hare a yankunan masarautar Kagoro da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar sojoji biyu tare da wasu da dama, lamarin da ya bayyana a matsayin "mai tashin hankali."

Buhari ya yi wadannan kalamai a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar wacce Muryar Amurka ta sami kwafi .

“Harin da matsoratan suka kai kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, da kan jami’an tsaro da lalata gidaje da shaguna, abu ne mai matukar zafi da kuma cin rai. Mu al’ummar kasar baki daya na jimami da al’ummar Kagoro, inda aka kai hare-haren da sojoji da suka rasa jajirtattun ‘yan uwansu,” in ji Shugaban.

Shugaba Buhari ya ce yana matukar bibiyar matakan da gwamnatin jihar Kaduna da jami’an tsaro ke dauka domin zakulo maharan da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

Ya kuma yi gargadin a guji ramuwar gayya da ka iya haifar da tashin hankali.

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG