Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi Tur Da Asarar Rayuka A Jihar Filato


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

A wata sanarwar da kakakin shugaban, Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya nuna takaicinsa kan yadda rai ba komai ba ne a Najeriya a yayin da jama’a ke ci gaba da rasa rayukansu a kasar inda a karshen mako, mutane 86 suka hallaka a Jihar Filato bayan da rikici ya barke a karamar hukumar Barikin Ladi.

“Mun sani cewa akwai matsalolin yanayi da tattalin arziki da ke ruruta rikicin makiyaya da manoma. Sai dai mun san cewa akwai ‘yan siyasan da ke fakewa da wannan domin cimma burinsu.”inji Buhari

Ya kuma gargadi jama’a da gujewa daukan doka da hannunsu sannan kuma ya ce za a bi a hukumta duk wadanda ke da hannu a cikin rikicin.

Rikicin dai ya samo asali ne tsakanin Fulani makiyaya da manoma, inda kowa ke zargin kowa da kai hare-haren da yayi sanadiyyar hallaka rayuka.

Yanzu dai abu ya lafa a cewar Kakakin rundunar tsaro ta STF a Jihar Filato, Manjo Umar Adam. Ya ce tashin hankalin ya faru ne sanadiyar harin da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka kai kan wasu kauyuka. Bayan da ‘yan sanda suka ji karar bindiga sai suka je wurin suka kuma tarar da mutanen har suka mayar da martani.

Kawo yanzu mutane 86 aka ce sun rasa rayukansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG