Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Babban Taron APC Da Sabbin Shugabanni


Babban Taron APC a Abuja

Jam’iyya mai mulki a Najeriya APC ta kammala babban taron da ta yi a Abuja inda ta sake zabar sabbin shugabaniin da zasu gudanar da al’amuran jam’iyyar.

Babban taron jam’iyyar APC ya kammala da manyan kujeru suka samu ta hanyar janyewa, inda sabon shugaban jam’iyyar Adams Oshiomohole ya samu nasara babu hamayya, shi kuma sakataren jam’iyyar Mai Mala Buni ya koma kujerarsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tafi da murmushi baya ga kiran wadanda suka yi fushi da su yi hakuri.

Daya daga cikin wakilan taron, Aminu Dan Arewa, ya nuna jin dadinsa ga yadda shugaban kasa ya koma gefe ya bayar ‘yan jam’iyyar su zabi wadanda suke ganin zasu iya tafiyar da jam’iyyar.

Yayin da ba a ga wasu dake cikin Majalisar Dattawa na sabuwar PDP a taron ba, shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da na Wakilai Yakubu Dogara sun halarci taron.

Sakataren jam’iyyar APC Mai Mala Buni, ya yi alwashin yin adalci tare da cewa wannan nauyi da Allah ya daura musu zasu yi iya bakin kokarinsu.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG