Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Zai Tafi Gambia Wajen Bikin Rantsar Da Shugaba Adama Barrow


Shugaba Buhari ((Facebook/Femi Adesina))
Shugaba Buhari ((Facebook/Femi Adesina))

Kazalika bikin zai samu halartar wasu shugabannin kasashen nahiyar Afirka in ji sanarwar ta Garba Shehu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kama hanyar kasar Gambia a yau Laraba don halartar bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow a wa’and mulki na biyu.

Wata sanarwa da kakakin Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar ta ce shugaba Barrow ne ya gayyaci Buhari wajen bikin rantsarwar wanda za a yi a Banjul babban birnin kasar

Kazalika bikin zai samu halartar wasu shugabannin kasashen nahiyar Afirka in ji sanarwar ta Shehu.

“Shugaba Buhari tare da sauran shugabannin ECOWAS sun taka rawar gani wajen maido da kasar ta Gambia kan tafarkin dimokradiyya a shekarar 2017, bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jameh ya ki amincewa da kayen da ya sha a zaben kasar da aka yi.” Sanarwar ta kara da cewa.

A cewar Shehu, Buhari zai samu rakiyar Ministan kula da harkokin kasashen waje Mr Geoffrey Onyeama da mai ba da shawara kan tsaron kasa Manjo-Janar Babagana Monguno sai Darektan ma’aikatar tattara bayanan sirri ta kasa Ambasada Ahmed Rufa’i da sauran manyan jami’an gwamnati.

“Shugaba Buhari zai koma Najeriya da zarar an kammala bikin rantsarwar.” Sanarwar ta ce.

XS
SM
MD
LG