Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukin Tuna Harin Da Kasar Japan Ta Kaiwa Amurka Shekaru 75


A yau laraba ake gudanar da babbar haduwa ta karshe ta wadanda suka kubuta da rayukansu daga farmakin da kasar Japan ta kai kan tashar jiragen ruwan Pearl Harbor a Hawaii, shekaru 75 cur bayan wannan harin da ya sa ita ma Amurka ta shiga cikin yakin duniya na biyu.

Abubuwan da za a yi sun hada har da zaman tsit a daidai lokacin da jiragen saman yakin Japan suka fara ruwan bam da ya kashe mutane kusan dubu 2 da dari 4, akasarinsu sojojin ruwa na Amurka. Hari la yau akwai bukin aza furanni da wasan badujala da kuma shawagin jiragen sama irin na wancan zamani.
Wani abin tarihi kuma zai faru kwanaki 20 bayan wannan buki a sansanin mayakan ruwan, a lokacin da Shinzo Abe zai zamo firayim ministan Japan na farko da zai ziyarci wurin tunawa da wadanda suka mutu a wannan farmaki ta sama da kasarsa ta kai. Sai dai kuma kuma wadanda suke sa ran cewa firayim ministan na Japan zai nemi gafara, hakarsu ba zata cimma ruwa ba.
Sakataren majalisar zartaswar kasar Japan, Yoshihide Suga, ya fada a birnin Tokyo cewa makasudin wannan ziyara da Mr. Abe zai kai shine karrama wadanda suka mutu, ba wai bayar da hakuri ba.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG