Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gangamin Tabbatar Da Babu Magudi A Zaben Amurka


Masu neman a sake kirga kuri'un zaben Amurka

A wajen ginin hada-hadar kasuwancin Trump, inda layin 5th avenue da 56th street suka hadu a birnin New York, an ji hayaniya da sanyin safiyar yau, yayin da masu goyon bayan a sake kirga kuri’un jihohi 3 suka hadu da ‘yar takatar jam’iyyar Green Party, Jill Stein a wani gangamin tabbatar da cewa babu magudi a kirgan kuri’un da akayi.

“Mun zo nan ne don mu tabbatarwa Trump cewa kada ya karaya”, a cewar Ms. Stein. In dai ka yarda da dimokradiyya, in kuma ka yarda da tabbacin nasarar ka, to ka ajiye makamanka, ka kawas da duk wani dogon turanci, ka kawo karshen razanawar da ka keyi ka zo ka hada hannu da Amurkawa dake neman dimokradiyyar da zata amfani kowa da kuma zaben da zamu iya amincewa da shi.

Masu zanga-zanga sun katse gungun magoya bayan dake waka suna maganganu. “kada kuri’a ba bisa ka’ida ba, an bar yara a baya, Stein ba zata canza sakamakon zabe ba: sai an rantsar da shugaba Trump ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2017.

Wani alkali ya bada umurnin a sake kirga kuri’u da hannu a jihar Michigan, daya daga cikin jihohin da aka fafata da Stein ta yi imanin cewa an yi magudi saboda na’urorin da aka yi amfan ida su sun tsufa, haka kuma ta na neman kotun tarayya ta bada umurnin a sake kirga kuri’u a jihar Pennsylvania.

XS
SM
MD
LG