Accessibility links

Karamin Ministan Ma'aikatar Kiwon Lafiya Dr Ali Mohammed Pate ya yi murabus

Ministan kasa a ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya Dr. Ali Mohammed Pate ya yi murabus domin kama aikin koyaswa a wata jami'a a Amurka.

Ministan Dr Ali Mohammed Pate ya ce babu wata takaddama ko wani rashin jituwa tsakanin shi da shugaban kasa. Ya ce shugaban kasa ya amince masa ya kama aikin koysawa da ya samu da wata jami'a a Amurka kuma ya amince masa da ya cigaba da zama shugaban kwamitin na musamman na shugaban kasa na yaki da cutar shan inna da sauran cututuka dake addabar yara. Har wa yau shugaban kasa ya yaba masa da aikin da ya yiwa Najeriya.

Da yake mayarda jawabi ministan ya ce ya godewa shugaban kasa da ya bashi zarafi ya yiwa Najeriya aiki. Ya ce kome na da nashi karshen hatta ma rayuwa. Amma ya ce zai cigaba da tallafawa kasar domin ya tabbatar cewa nasarar da aka samu ba'a yi asararta ba. Da aka tambayeshi yadda zai cigaba da aikin kwamitin shugaban kasa yayin da yake malunta a kasar waje sai ya ce duniya ta zama karamar kasa sanadiyar yanar gizo. Ya ce yana iya koyaswa ko'ina yake a duniya har da aikin kwamitin ba tare da wata matsala ba.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

XS
SM
MD
LG