Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buratai Ya Zama Jakadan Najeriya A Jamhuriyar Benin


Buratai (hagu) da Minista Onyeama (dama) (Facebook/Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya)

Kazalika, an nada Janar Abayomi Gabriel Olonisakin mai ritaya wanda shi ne tsohon hafsan hafsoshin Najeriya a matsayin jakadan kasar a Kamaru.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Laftanar-Janar Yusuf Buratai mai ritaya, a matsayin jakadan kasar a Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da Najeriyar.

Buratai shi ne tsohon babban hafsan sojin kasa na Najeriya wadanda aka sauke su a watan Janairun bana.

Kazalika, an nada Janar Abayomi Gabriel Olonisakin mai ritaya wanda shi ne tsohon hafsan hafsoshin Najeriya a matsayin jakadan kasar a Kamaru wacce ita ma makwabciya ce ga Najeriyar.

Olonisakin (hagu) Onyeama (dama) (Facebook/Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya)
Olonisakin (hagu) Onyeama (dama) (Facebook/Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya)

A wani dan kwaryakwaryan biki da aka yi a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya a Abuja, Minista Geoffery Enyeama ya mikawa Buratai da Olonisakin wasikun tabbatar masu da mukamansu.

Tun dai a watan Fabrairun da ya gabata, Shugaba Buhari, ya mika sunayen tsoffin manyan hafsoshin sojin kasar hudu ga majalisar dokoki don a tantance su a matsayin jakadu.

Sauran biyun sun hada da Vice Adminiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya da Air Marshal Sadique Abubakar mai ritaya

Amma ya zuwa yanzu Buratai da Olonisakin kawai aka nada.

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG