Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cacar Baki Tsakanin PDP Da Fadar Shugaban Najeriya Kan Zargin Yunkurin Kifar Da Gwamnati


PDP, Shugaba Muhammadu Buhari.
PDP, Shugaba Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta maida martani akan ikirarin fadar shugaban kasa, cewa wasu ‘yan kasar na kokarin kifar da gwamnati ta hanyar da ta sabawa tsarin dimokaradiyya.

Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasa Femi Adesina ya fitar a jiya Talata, ta yi zargin cewa wasu shugabannin addini da wasu tsoffin shugabannin siyasa na kokarin ta da zaune tsaye da kuma kokarin ganin bayan gwamnatin shugaba Buhari ta kowane hali.

Sanarwar ta fadar shugaban kasa ta ce daga cikin tsare-tsaren na su, sun shirya gudanar da wani taron kasa ba bisa ka’ida ba inda za su kada kuri’ar kin jinin shugaba Buhari, tare da manufar kifar da gwamnatinsa.

Buhari, dama da Femi Adesina, hagu (Facebook/Femi Adesina)
Buhari, dama da Femi Adesina, hagu (Facebook/Femi Adesina)

Fadar ta shugaban kasa wadda ke kafa hujja da wani gargadi da hukumar tsaro ta DSS ta fitar, ta kara da cewa masu yunkurin ganin an sauya gwamnatin da “karfin tuwo” suna kokari ne su aiwatar da hakan saboda gazawar da suka yi a zaben 2019.

To sai dai da take maida martani, jam’iyyar adawa ta PDP, ta bayyana zarge-zargen na fadar shugaban kasa a zaman “wani yunkuri na shafawa wasu kashin kaji a lokacin da gwamnati ta gaza.”

Karin bayani akan: Femi Adesina, APC, PDP, DSS, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A cikin wata sanarwa da kakakinta na kasa Kola Ologbondiyan ya fitar, jam’iyyar ta PDP ta zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC, da kokarin boye kasawarta a kan alkawuran da ta yi wa ‘yan kasar a lokacin yakin neman zabe.

A cewar PDP, "maimakon fadar ta shugaban kasa ta himmatu wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da tsaron kasa, sai kawai ta maida hankali wajen yin zarge-zargen da ba su da tushe balle makama ga ‘yan Najeriya."

Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP
Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP

Ta kara da cewa wannan zargi na fadar shugaban kasa, yunkuri ne kawai na jam’iyyar APC domin kara zafafa al’amuran zaben 2023 mai zuwa “a yayin da suka gane cewa ba za su iya tunkarar jama’a ba a lokacin zaben.”

To sai dai kuma sanarwar ta PDP ta tunatar da shugaba Buhari abin da ya wakana a shekarar 1983, sa’adda “ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da zababbiyar gwamnatin dimokaradiyya a wancan lokacin.”

Jam’iyyar ta PDP ta jaddada cewa kamar kowane dan kishin kasa, tana ci gaba da goyon bayan dorewar dimokaradiyya, hadin kai da kuma ci gaba da wanzuwar Najeriya a zaman kasa daya.

Sanarwar ta fadar shugaban kasa dai ta biyo ne bayan wata sanarwar ankararwa da hukumar tsaro ta DSS ta fitar, da ke nuna cewa akwai wani yunkuri na hambarar da gwamnati ba bisa tanadin tsarin dimokaradiyya ba a kasar, zargin da ya hada har da wasu shugabannin addini.

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, ta yi kiran da a zurfafa bincike akan zarge-zargen na fadar shugaban kasa, tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

To sai dai ita ko kungiyar Kiristoci ta Najeriya, ta yi watsi da sanya bangaren addini a cikin zargin na fadar shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG