Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kada A Saka Dokar Ta-Baci a Najeriya - Masari


Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari (Twitter/@GovernorMasari)

Kalaman Masari na zuwa ne, kwana biyu bayan da majalisar wakilai ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana dokar ta baci a fannin tsaron kasar.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce saka dokar ta baci a fannin tsaron Najeriya ba ita ce mafita ga matsalolin da suka addabi kasar ba.

A cewar Masari, babu jihar da babu sojoji a cikinta a yanzu haka, yana mai cewa saka dokar ta bacin ba za ta magance matsalolin ba.

“Sojojin namu nawa ne? gaskiyar magana ita ce, nauyin samar da zaman lafiya a kasar nan, ya rataya ne a wuyan kowa da kowa.” Masari ya fadawa manema labarai a ranar Alhamis, bayan wata ganawa da suka yi da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari.

Kalaman Masari, wanda tsohon kakakin majalisar wakilai ne, na zuwa ne kwana biyu bayan da majalisar ta wakilai ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana dokar ta bacin.

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila (Instagram/speakergbaja)
Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila (Instagram/speakergbaja)

Majalisar ta dauki wannan matsaya ce, bayan da gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta mamaye wasu yankunana karamar hukumar Shiroro.

“Ina mai tabbatar muku da cewa, akwai ‘yan Boko Haram a Kaure da ke nan jihar Neja. Kuma har sun kafa tutarsu.” Gwamna Bello ya ce.

Wacce Irin Rawa Amurka Za Ta Iya Takawa?

Yayin wata ganawa ta yanar gizo da suka yi da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a ranar Talata, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nemi taimakon Amurka kan matsalar tsaron da ta addabi kasarsa.

Shugaban ya nemi Amurkar ta maido da hedikwatar rundunar wanzar da zaman lafiya a Afirka ta sojojin AFRICOM zuwa nahiyar Afirka.

Shugaba Buhari, yayin da suke taro da Sakataren Harkokin wajen Amurka, Antony Blinken (Twitter/@bashiraahmad)
Shugaba Buhari, yayin da suke taro da Sakataren Harkokin wajen Amurka, Antony Blinken (Twitter/@bashiraahmad)

Hedikwatar rundunar na birnin Stuttgart ne da ke kasar Jamus a yanzu haka.

“Kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya, babban abin damuwa ne, saboda abubuwan da ke faruwa a yankunan Sahel, tsakiya da yammacin Afirka da kuma yankin Tafkin Chadi.” Wata sanarwa da kakakin Buhari Garba Shehu ya fitar bayan taron ta ce.

Karin bayani akan: Aminu Bello Masari, AFRICOM, IPOB, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.

Buhari ya kara da cewa, Najeriya da jami’an tsaronta, sun himmatu wajen ganin sun shawo kan musabbabin wadannan matsaloli duk da irin girmansu.

Amma, “goyon bayan muhimman kawaye irinsu Amurka, abu ne da ba za a gaji da nanatawa ba, saboda sakamakon da rashin tsaro zai haifar, zai iya shafar dukkan kasashe.”

Abin Da Atiku Abubakar Ya Ce

Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da bayyana ra’ayi mabanbanta, kan yadda za a shawo kan matsalar tsaron kasar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi gargadi kan abin da rashin tsaron zai iya haifarwa kasar.

A wani sakon Twitter da ya wallafa a shafinsa, Atiku ya ce, idan Najeriya ba ta magance matsalar tsaron ba, babu shakka, matakan da ake dauka don tsamo kasar daga kangin da ta shiga duk za su ruguje.

“Matsalar rashin aikin yi za ta yi kamari, talauci zai kara yi wa mutane katutu.” In ji Atiku

“Babu shakka, matsalolin da muke fuskanta suna da girma, amma za a iya shawo kansu. Abin da muke bukata shi ne, shugabanci da kuma himma wajen yin abin da ya fiyewa kasarmu da al’umarmu,” tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2019 ya ce.

Najeriya ta jima tana fama da matsalar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, matsalar da ta kara ta’azzara a ‘yan kwanakin nan.

A makon da ya gabata, mayakan na Boko Haram da na ISWAP, sun kai hare-haren a jihohin Borno da Yobe da ke makwabtaka da juna.

A Borno, rahotanni sun ce mayakan sun karbe ikon garin Mainok, ko da yake rundunar sojin Najeriya ta musanta wannan ikirari.

Sabbin Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya
Sabbin Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya

A Yobe kuwa, ‘yan bindigar sun tarwatsa garin Giedam inda suka jefa dubun dubatar mutane cikin kangin yin kaura, bayan jerin kwanaki da suka kwashe suna kai harin a garin.

A arewa maso yammaci, ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, sun addabi yankin inda sukan kai hare-hare akan kauyuka da makarantu tare da sace dalibai ciki har da na jami’a.

Ko a makon da ya gabata, an kashe gomman mutane a wasu kauyukan jihar Zamfara bayan da wasu mahara suka kai cafka akan wasu kauyukan jihar.

A baya-bayan nan, wasu ‘yan bindiga sun sace dalibai a jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna, inda suka kashe biyar daga cikinsu bayan da suka nemi a biya su miliyan 800 a matsyain kudin fansa.

A kudancin kasar, baya ga satar mutane da ake yi, ‘yan bindiga sun dauki salon kai hare-hare akan jami’an tsaro da ofisoshinsu musamman a kudu maso gabashi.

Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra, IPOB
Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra, IPOB

Sannan ga rikicin ‘yan awaren kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra da ake zargi da kai hare-hare, zargin da suke musantawa.

Shugaban kasa Buhari ya sha ba jami’an tsaron kasar umurnin su farauto masu kai wadannan hare-hare, amma kamar yadda rahotanni ke nunawa, lamarin bai sauya ba.

Hakan ya sa a ‘yan kwanakin nan, wasu ke kiraye-kirayen ya sauka a mulki ko a tsige shi yayin da wasu ke cewa a ayyana dokar ta baci a kasar.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG